Tarihin Gwamnan Farko Na Jihar Katsina Manjo Janar Abdullahi Sarki
LManjo Janar Abdullahi Sarki Muktar (RTD.), LLB, ABU, An haife shi kuma ya tashi ne a Unguwar Soron Dinki, cikin birnin Kano. A lokacin yana Kanal, shi ne gwamnan farko na sabuwar jihar Katsina a shekarar 1987, wadda aka karkasa daga tsohuwar jihar Kaduna ta hannun Shugaban Ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Daga baya aka canja masa wuri, aka naɗa shi gwamnan Jihar Kaduna daga Yuli 1988 zuwa Agusta 1990. Ta hanyar jarabawa da horo mai zurfi da ya yi a Najeriya da ƙetare, ya ci gaba da tashi har ya kai matsayin Manjo Janar. A mulkin Janar Sani Abacha, an naɗa shi GOC Kaduna, wato babban kwamandan rundunar Sojin Najeriya a yankin. A cikin shekarun 1980s, ya ci gaba da karatunsa, inda ya yi horo na shekaru biyar domin yin LL.B a jami’ar Ahmadu Bello University (ABU) Zaria, cibiyar ilimi mafi girma a Arewacin Najeriya, wadda aka kafa a ranar 4 ga Oktoba 1962 ta jagorancin hazikin jagora Sir Ahmadu Bello, KBE, Firayim Ministan Arewa. Kafin rasuwar Janar Abacha a ranar 8 ga Yuni 199...