Yadda Zaka Nemi Kudi Online a Cikin Watan Ramadan
A matsayinka na Freelancer a bangaren Technology wanda yake neman kudi a online, wanda sai ya bude data yake samun na kashewa, ga wani tsari da zaka bi a watan Ramadan mai albarka.
Zaka mayar da daren watan Ramadan ya zama lokacin ibadar ka, zaka rika tashi da misalin karfe 3:00am na dare domin yin Tahajjud, kayi raka’o’i gwargwadon hali, ka yawaita istighfari da addu’o’i musamman kan neman yafiyar ubangiji, neman Aljanna da fatan cikawa da imani da kuma yiwa iyaye addu'a da rokon Allah ilimi mai Albarka da addu'o'in kara Albarka ga sana’a da neman halal.
Bayan haka zaka dauki lokaci kana karatun Al-Qur’ani cikin natsuwa, bawai kuma kawai karantawa ba, ya zama kana karanta shi da tadabbur domin fahimtar ma’anar abinda kake karantawa.
Bayan Suhoor da Sallar Asuba a masallaci, zaka zauna kayi adhkar na safe sannan ka tsara manyan abubuwa uku da kake son cimmawa a wannan ranar farkon.
A bangaren aiki ko neman kudinka na Internet, zaka ware mafi kyawun lokaci daga karfe 8 na safe zuwa 11 na safe domin gudanar da manyan ayyukan freelancing da kakeyi, walau coding, security testing, bug hunting, da rubuta proposals ga clients da sauransu.
Ramadan ba lokacin yin aiki mai yawa ba ne, amma lokacin yin aiki mai kyau ne domin samun abinda zaka rufa ma kanka asiri, neman halal ma ibada ne idan an gyara niyya.
Bayan haka zaka dan huta kadan daga harkokin online. Bayan Sallar Zuhr, zaka dauki lokaci kadan kana karatun Qur’ani ko sauraron wani wa'azi na addini daga wani malamin addinin, idan akwai bukatar karatu a bangaren da kake karatu na Tech, zaka yi shi a wannan lokacin bayan ka gama sauraren wa'azin, ko kuma ka samu kayi bacci na dan lokaci.
Da yammaci bayan Sallar Asr, zaka kara komawa ga Al-Qur’ani ko adhkar, sannan ka duba emails dinka ko kuma fara shirya ayyukan da zaka gudanar a gobe.
Gaf da Maghrib, zaka maida shi lokacin addu’a, domin yana daga cikin lokutan da ake fatan karÉ“uwar addu’a. Zaka roki Allah ya sanya albarka a iliminka da sana’arka, da rayuwarka bakidaya.
Bayan Iftar da Sallar Maghrib, zaka halarci Tarawih a masallaci. Daren Ramadan ba ya cika sai da tsayuwa a gaban Allah. Bayan dawowa gida, zaka rage amfani da wayar hannu da social media mara amfani, ka dauki lokaci kadan tare da iyali, sannan ka kwanta da wuri domin sake tashi don Qiyamul Lail.
Wannan tsarin zai koya maka cewa Ramadan wata ne na gyaran zuciya da inganta kai, ka maida data da internet kayan aiki na alheri, ba kayan bata lokaci ba. Ka maida neman kudin halal ibada. Ka maida ilimi sadaka.
Idan muka tsara rayuwarmu a Ramadan da tsari da niyya mai kyau, za mu iya fita daga watan ba kawai da ladar azumi ba, har da karin ilimi, karin kwarewa, da karin kusanci ga Allah.
Allah ya bamu ikon cin gajiyar watan Ramadan, ya sanya mana albarka a cikin lokaci da ayyukanmu. Amin

Comments
Post a Comment